YA KAMATA GWAMNATOCIN AREWA SU TALLAFA WA RUBUTU DA MARUBUTA HAUSA ~ AUYO
Auyo matashin marubuci ne da yayi tashe a lokacinsa, salon rubutunsa ya sha bambam da rubutun mafi akasarin Marubuta. ya fara rubutu tun yana da shekara goma sha uku a duniya kuma har ila yau yana rubutu mai cike da fad'akarwa, ilmantarwa gami da Nishad'antarwa. Littafinsa HISABI na d'aya daga cikin tarin littafan da Makaranta ke tsumaye. Ga hirarsa da Mujallar Fikra
***
***
Mujallar
Fikra: Assalamu
Alaikum warahmatullah
Auyo: Waalaikumus salam wa
rahmatullahi wa barakatuhu
Mujallar
Fikra: Zamu so mu ji takaitaccen tarihinka
Auyo: Cikakken
sunana Abubakar Muhammad . An haife Ni a garin Auyon Jihar Jigawa, na yi makarantar
firamare a nan daga nan na tafi garin Aujara in da na yi karamar makarantar
kimiyya da fasaha, bayan na kammala na dawo babbar makarantar kimiyya da fasaha
ta garin kafin Hausa. Na kammala a shekarar 2006, in da na shiga makarantar
koyon aikin jinya ta garin Jahun a shekarar 2007. Na kammala a 2010, na
yi aiki na wucin gadi da kungiyar lafiya ta duniya a 2011 kafin a 2012 na samu
aiki na din-din-din a ma'aikatar lafiya ta Jihar Jigawa. A 2016 na samu gurbin
ci gaba da karatu a kasar India daga baya na samu a Kenya, in da na za6i tafiya
kasar Kenya, yanzu Ina nan ina karantar Bsc Medical Lab. Science.
Mujallar
Fikra: Baka faɗa
mana shekarunka ba.
Auyo: An haife Ni a cikin
shekara ta 1991, yanzu Ina da shekaru 26 kenan.
Mujallar
Fikra:: Yaushe ka
fara rubutu?
Auyo: Na fara a 2004.
Mujallar
Fikra: Lokacin
kana wani mataki na karatu?
Auyo: Lokacin ina SS 1
Mujallar
Fikra:: Mai ya ja
hankalin ka fara rubutu?
Auyo: Kasancewa ta mai son
karatun littafan hausa, wannan ne ya d'an sa min sha'awar nima na Zama
marubuci. Daga nan na fara.
Mujallar
Fikra:: MaashaAllah,
fara rubutu a aji huɗu na sakandire na nufin ka taso da ra'ayin yin rubutu. Da
wani labari ko in ce littafi ka fara?
Auyo: Na fara da wani da
na masa suna MALLAKAR MIJI a bisa jigon zamantakewar ma'aurata
Mujallar
Fikra: Me ya ɗauki
hankalinka kayi rubutu akan zamantakewar ma'aurata a wannan lokacin
Auyo: Wannan rubutun na yi
shi ne bayan nazartuwa da rashin hakuri, da kuma mayar da karamin laifi babba a
tsakanin ma'aurata, da kuma kuskuren wasu matan na mijinsu ya so ya kuma kula
su kadai kawai ya bar 'yan uwansa da wasu na kusa da shi.
Mujallar
Fikra:: Shin
littafin ya samu karɓuwa lokacin?
Auyo: Fara rubutu daban,
fitar da littafi daban, in fitar da littafi ne a 2013 na fara.
Mujallar
Fikra: OK! Mun ɗauka ka fitar da Mallakar mijin ne.
Auyo: A'a ba shi na fitar
ba, Madubi Sha Kallo na fitar.
Mujallar
Fikra: Baka da
ra'ayin fitar da shi ne ko sai a gaba?
Auyo: Gaskiya bani da
ra'ayin fitar da shi, hasali ma lokacin ina rubutu ne a kan takarda, lalubensa
a yanzu zai matukar ban wahala, baya da haka tunanina na shekarun can da na
yanzu da bambanci. Ina ga kamar an yi rubutu da yawa a kan irin wadannan
matsalolin, hasali ma dai su suka fi yawa. Saboda haka Ni ma ya kamata na dau wani
6angaren
Mujallar
Fikra: Shi
Madubin me ya kunsa, zaka iya bamu takaitaccen bayani akan sa
Auyo: Madubi, labari ne na
wani hazikin matashin bakauye mai suna HAFIZU da yake karatu a kwalejin
ilimi, ba tare da lura da talaucinsa ba yayi amfani da basirarsa wajen
yaudarar 'yam Mata, a karshe ya yiwa wata ciki, suka ribace ta shi da abokinsa
suka Kai ta jeji suka aikata Mata aika-aika, sa'an Nan suka tona Rami suka
binneta da zaton ta mutu.
Daga Nan suka dawo, rayuwa ta ci gaba da garawa, yarinyar da suka binne ta samu ceton daga wani bafulatani.
A yaudare-yaudarensu HAFIZU ya hadu da aljana, ya kamu da yoyon fitsari.
A karshe dai asirinsu ya tonu, suka shiga gidan maza.
Daga Nan suka dawo, rayuwa ta ci gaba da garawa, yarinyar da suka binne ta samu ceton daga wani bafulatani.
A yaudare-yaudarensu HAFIZU ya hadu da aljana, ya kamu da yoyon fitsari.
A karshe dai asirinsu ya tonu, suka shiga gidan maza.
Mujallar
Fikra: Ya kake
haɗa rubutunka da karatu da aikin ka ganin abin da ka karanta ko kusa bai da
alaka da rubutu
Auyo: Kowanne ina tsara
shi, lokacin da ina gida ba ko yaushe nake aiki ba, kasancewata Mai son kadaici
wannan ya ba ni damar zama Ni kadai na yi rubutu a duk ranar da ba na aiki,
haka ma dai a yanzu da nake makaranta ina da lokacin da nake rubutu
Mujallar
Fikra: Zuwa
yanzu littafai nawa ka rubuta kuma nawa ka fitar
Auyo: Wadanda na yi typing
akwai akalla bakwai, wadanda suka fita kuma uku ne.
Mujallar
Fikra:: Wanne ka fi
so?
Auyo: Wanda na fi so bai
fita ba, sunansa HISABI, na rubuta shi ne a Nan, Mai yiwuwa in na koma gida na
hau aikinsa gadan-gadan
Mujallar
Fikra: Wanne
ya fi karɓuwa?
Auyo: Kowanne ya amsu,
amma littafina na farko kasancewar shine ya fito da ni a duniyar rubutu
Mujallar
Fikra: Zaka so
a fassara littafanka zuwa nai halshe?
Auyo: Kwarai kuwa, nima
ina da sha'awar na yi rubutu a wani harshen da ba na Hausa kawai ba
Mujallar
Fikra: Wani
mataki kake ganin rubutu da marubuta hausa suka taka a duniyar adabi
Auyo: Matakin a ganina
shine bai wuce na yawaitar marubuta ba, amma idan aka kwatanta marubutanmu da
marubutan sauran kasashe gaskiya an bar mu a baya, ko da yake a yanzu ana
kokari wajen yin bincike
Mujallar
Fikra: Shin
akwai wata matsala da ke addaban duniyar ta su?
Auyo: Kwarai, akwai
matsaloli. Na farko shine na kasuwanci , duk wanda ya buga littafi tunaninsa
bai wuce ya Kai shi tsukakkiyar kasuwar sayar da littafi ta sabon gari da kuma
kasuwar kurmi ko bakin asibiti ba a danka ma dillalai sai yadda suka yi da shi.
Da yawa ana rubutu ne kawai saboda sha'awa da kuma kudirin Rai, a yayin da wasu kasashen sauran marubuta ke kwasar miliyoyi, hasali ma dai rubutun ne sana'arsu.
Da yawa ana rubutu ne kawai saboda sha'awa da kuma kudirin Rai, a yayin da wasu kasashen sauran marubuta ke kwasar miliyoyi, hasali ma dai rubutun ne sana'arsu.
Mujallar
Fikra: A
matsayin ka na marubuci Madubin al'umma me zaka ce da matasan Kasar Hausa?
Auyo: Yanayin yadda
matsanmu suke abu ne Mai daga hankali gaskiya, yawan matasa a kasa arziki ne da
gwamnati za ta iya amfani da shi wajen ciyar da kasa gaba, Amma sabanin haka a
wajen shugabanninmu matasa ba su wuce wad'anda za su na musu ihu ba a yayin
za6e da kuma a kafafen sada zumunta na zamani, yayin da 'ya'yansu ke karatu.
.
Sa'an Nan kuma matasa mu dage da karatu, kuma mu yi kanmu gatan dagewa a kan sana'a komai kankantarta, kuma kar mu dogara da cewa in mun yi karatu sai gwamnati ta ba mu aikin yi, qila da zamu zauna mu yi tunani za mu iya samowa kanmu wani aikin da ba lallai aikin gwamnati ya bamu abun da za mu samu a ciki ba
.
Sa'an Nan kuma matasa mu dage da karatu, kuma mu yi kanmu gatan dagewa a kan sana'a komai kankantarta, kuma kar mu dogara da cewa in mun yi karatu sai gwamnati ta ba mu aikin yi, qila da zamu zauna mu yi tunani za mu iya samowa kanmu wani aikin da ba lallai aikin gwamnati ya bamu abun da za mu samu a ciki ba
Mujallar
Fikra:: Wace mataki
kake fatan Adabin hausa ta kai?
Auyo: Ina fatan a ce ya
Kai duk wani mataki da adabi yake Kai wa a duniya.
Mujallar
Fikra:: Wace
shawara zaka ba gwamnati dangane da rubutu da marubuta Hausa
Auyo: Gaskiya shine
marubuta suna da rawar takawa sosai a cikin al'umma ta 6angaren zamantakewa da
kuma wayar da Kai, da a ce gwamnatocinmu sun lura da haka to da marubuta ba
karamin aiki za su rage rage musu ba.
.
Yana da kyau gwamnatocinmu su karfafawa marubuta gwuiwa ta hanyar tara bitoci, tallafawa ta hanyar inganta labaransu , kaifafa tunani da kuma buga littafan a ingataccen bugu da za a iya dagawa a ko ina a duniya.
.
Yana da kyau gwamnatocinmu su karfafawa marubuta gwuiwa ta hanyar tara bitoci, tallafawa ta hanyar inganta labaransu , kaifafa tunani da kuma buga littafan a ingataccen bugu da za a iya dagawa a ko ina a duniya.
Mujallar
Fikra:: Wani kira
kake ga maluma da sarakuna game da tallafin da zasu ba harkan rubutu. Don sau
da yawa zaka ji maluma suna kushe harkan shin ko menene dalili sannan me hakan
ke jawowa ga cigaban adabi?
Auyo: Sarakuna suna ba
marubuta goyon baya kwarai, saboda a taruka suna amsa gayyata , ba da gudunmawa
da kuma tura wakilai in suna da uzuri. Malamai kuma kowa yana da ta sa fahimtar
a rubutu, wasu suna kallon sassaukar hanya ce ta isar da sako, wasu Kuma suna
kallon cewa marubuta suna rusa tarbiyya , koma yaya ne dai kirana ga marubuta
shine mutum ya rubuta abun da yake da dalilin da zai iya Kare kansa.
Mujallar
Fikra:: Me zaka ce
da masoyanka
Auyo: Masoyana na gode,
kuma muna rubutu ne don ku, a duk wasu kurakurenmu a yi kokarin nusar da mu, ba
yabo kawai muke bukata ba
Mujallar Fikra:: Mun gode kwarai da amsa gayyata

Masha Allah, Allah Ya taimaka Ya bada sa'a Auyo. Allah Ya bamu ikon rubutu mai amfani.
ReplyDelete