YAWAN 'DAUKAKA LAIFI DA MA'AURATA KE YI YA FI KOMAI HADDASA SAKIN AURE- Azeeza Idris
Azeeza Idris wacce aka fi
sani da Ummyasmeen musamman a kafar
sadarwa ta Instagram da kafar karanta littatafai ta duniyar gizo wato Wattpad. Marubuciya
ce da tauraronta ke haskawa saboda d’umbin fikrar da Allah ya ba ta. Ta ci
sarauniyar Marubuta Nigeria a Duniyar Wattpad sannan tana da dubban Makaranta
littafanta daga ko ina a fad’in duniyar nan. Ba a rubutu kad’ai ta shahara ba har
ma da fannin girke-girke. Ga hirarta da Mujallar Fikra..
Mujallar Fikra: Assalamu
Alaikum warahmatullah
Aziza Idris: Wa’alaikumus
salam Wa Rahmatullah
Mujallar Fikra: Za mu so sanin wacece Umm Yasmeen
Aziza Idris: Masha Allah, da farko dai sunana Azizah Idris Muhammad. An haife ni a jihar
Bauchi a ranar 06/10/1988. Amma ni asali 'yar jihar Gombe ce daga karamar
hukumar Yamaltu/Deba. Nayi karatun firamare a Abubakar Tafawa Balewa
University Staff School zuwa aji uku kafin muka koma Gombe inda na ci gaba daga
aji hudu a Gombe children and High School. Na samu gurbin shiga sabuwar
makarantar kwalejin tarayya na mata dake Bajoga a lokacin da aka bude
makarantar mune dalibai sahun farko (pioneers). Na kammala a shekarar 2005
inda a wannan shekarar na samu Remedial program a ATBU, saboda rashin fitowar
JAMB result dina. Yayin da ya fito wayam ba komai. Bayan nan na samu gurbin
shiga jami'ar A.T.B.U inda na karanta digiri a kimiyyar na'ura mai kwakwalwa na
kammala a shekarar 2012. Bayan na yi bautar kasa, na yi aiki na wucin gadi
da Society for family health inda na musu aikin Management Information system
consultant. Bayan na bar wurin ne a shekarar 2014 na koma A.T.B.U domin
zurfafa ilimi a bangarena dai har ila yau wato kimiyyar na'ura mai
kwakwalwa. A halin yanzu ina karatu da Islamic Online University a
tsarinsu na PGD inda nake karanta Islamic Psychology. Nayi aure a shekarar
2008, ina da yara uku, yanzu haka ina zaune a garin Gombe tare da iyalaina.
Mujallar Fikra: Yaushe
ki ka fara rubutu?
Aziza Idris: Na
fara rubutu a shekarar 2004 ni da kawata ce dai muke dan jagwalgwalenmu a
makaranta amma asalin kammalallen littafin da na fara rubutawa a 2006 na rubuta
shi sai dai ban kai ga buga shi ba har yau. Na barshi a matsayin labarina ni
kadai. Littafin da ma fara rubutawa ya shiga kasuwa a 2007 ne mai suna SAUYIN
SHIRI.
Mujallar Fikra: Lokacin kina wani
mataki na karatu?
Aziza Idris: Na rubuta shi ina 100 level a 2006 kenan amma bai ahiga kasuwa ba sai 2007
farko
Mujallar Fikra: MaashaAllah! Mai
ya ja hankalin ki zu wa ga fara rubutu?
Aziza Idris: Abin da
ya ja hankalina na fara rubutu shine a 2004 na karanta wani littafi mai suna A
Glimpse of Goodness. Ba akan littafin na fara karatu ba amma akan littafin naji
wannan zaburar na lallai nima na rubuta abunda zai amfani al'umma. Banda shi
akwai littafin Hattara Iyaye na Aunty Bilkisu Funtua; sakon da littafin ya isar
ya nuna min nima zan iya isar da sakonni ta hanyar rubutu. Wannan ne ya ja
hankalina ga rubutu.
Mujallar Fikra: Za
mu so mu ji abin da littafin ya k’unsa
Aziza Idris: Littafin
Sauyin shiri sassaukan labarine da ya shafi zamantakewar cikin gida amma
al muhim labarin yafi nuni da yanayin tarbiyyar yara, yanda rashin kula da
hakan yake zuwa ya shafi rayuwarsu a gaba kamar yanda dan uwan Sumayya da aka
musu baiko ya bata rawarsa da tsalle ya tafi ya barta saboda rudin rayuwa ya zo
daga baya yana dana sani bayan ta samu mai sonta na gaskiya har ma tayi
aurenta. Haka nan labarin ya nuna muhimmancin amincewa juna da yarda a
rayuwar aure duba da yanda ta kowani bangare ake kaiwa Sumayya da Al'ameen hari
a zamantakewarsu amma dake sun aminta da juna kuma sun fawwalawa Allah
lamuransu, wannan ya hana miyagun mutanen yin nasara akansu.
Mujallar Fikra: Ya
samu karɓuwa a lokacin? Ganin cewa shine littafinki na farko.
Aziza Idris: Idan
akayi la'akari da cewa farkon littafina ne a lokacin gaskiya zance ya samu
karbuwa don ba dayawa nayi shi ba. Kuma kafun shekara ta zagayo ya bace a
kasuwa bat!
Mujallar Fikra: MaashaAllah, ya kike haɗa rubutu, karatu, aiki da kuma sabgogin iyali?
Aziza Idris: Eh
to bazance akwai sauki ba, sai lokacin da mutum yake cikin abu zai san wuyarsa.
Amma a yanda nake al'amurana ina yin komai ne bisa tsari. A can sama ban
ambaci cewa ni Professional Chef bace. To bayaga karatu ina aiki a makarantar
da na bude na koyar da girke-girke wanda hadin gwiwa ne da kawata. Ina
tsara ayyukana ne bisa lokutan sallah. Daga Asuba zuwa wayewar gari da aikin da
nakeyi; Kamar girki da shirya yara da karatu na fannin ilimin
addini. Daga wayewar gari zuwa azahar ma haka. A wannan lokacin nake
kimtsa gidana bayan yara sun tafi makaranta sai nayi aikin rairaya (editing) na
duk aikin da nakeyi na rubutu a lokacin ko kuma na bazama yin waya da shiga
yanar gizo domin bincike kan abunda na saka a gaba a wannan lokacin.
Haka daga Azahar zuwa la'asar lokacin nake aiki a
makarantar girkina. Nakan taso da yamma to idan yara sun taso islamiyya daga
magariba zuwa isha lokacin da nake zama dasu kenan muyi karatu ko mu koyi sabon
abu. Bayan isha kuma muyi home work dinsu tsanani karfe tara sunyi bacci.
Shi kuma maigida daga karfe goma zuwa karfe sha daya lokacinsa ne. To
bayan sunyi bacci ne nake samun cikakken lokacin rubutu daga karfe goma zuwa
karfe sha biyu. Wataran ya tayani gadi wataran nace masa bana son yin magana
abubuwan zasu gudu hahahaha.
Ranar da babu islamiyya nima bana aiki kamar Asabar
haka sai muje muyi ziyarar 'yan uwa ko zuwa asibiti da yaran da mai
gidan.
Baccina daga sha biyu ne zuwa karfe biyar ko kuma
hudu da rabi nakanyi shekaru banyi baccin rana ko sau daya ba. Sai ko da
larurar rashin lafiya.
Mujallar Fikra: Littafai
nawa kika rubuta daga fara rubutunki zuwa yanzu?
Aziza Idris: Na
rubuta littafai guda ashirin da hudu. Biyu gajerun labarai ne ba
cikakken littafi ba. GUDAN JINI da ANYI BA AYI
BA.
Goma sha biyar sun shiga
kasuwa;
SAUYIN SHIRI
HALIN ZUCIYA
MY KITCHEN ESSENTIALS
HAR GABAN ABADA
DANDANON GIDA
SABUWAR RAYUWA
RIKITACCIYAR ALAKA
HUKUNCIN 'YA MACE
HALIN KO IN KULA
AALIYA
SURGEON's WIFE
AL'AMARIN ZUCI
AMAREN BANA
ZUBAR KWALLA
HALIN GIRMA
Biyu suna kan hanya In sha
Allah;
A SACK OF WISHES
UMM ADIYYA
A yayinda nake aiki akan
biyu yanzu ;
THE MECHANIC's WIFE
SHAMAKIN RAYUWA
Biyu kuma suna kammale amma
ban saka aikinsu a gaba ba;
BEING BILAAL's WIFE
KE NAKE SO.
Sai wanda na fara aikinsu
ban kammala ba;
MAIMAITA TARIHI
SHAMAKIN RAYUWA
UNNAMED.
Mujallar Fikra: A duk cikinsu wane kika fi so?
Aziza Idris: A
cikin littafn da nafi so gaskiya da wuya na iya zaba amma zan iya saka biyu? Aaliya
saboda shi ya kunshi sako mai muhimmanci na wayarda kan al'umma kan cutar daji
ta jini. Kuma wannan shine littafin da ya kara fito dani cikin al'umma sannan
akan littafin na kara horuwa da makaman rubutu wato kamar su bincike da
sauransu. Zubar kwalla kuma saboda yanda labarin ke nuni da asalin
tsagoron abunda rayuwar yanzu ke fuskantar barazanar tabarbarewar zumunci.
Shina mutane sun karbe shi sosai saboda duk mai karatu idan yaji labarin zaiji
ya tabashi donin tamkar da shi akeyi.
Mujallar Fikra: Wani
matsala kika taɓa fuskanta a duniyar rubutu kuma ta yaya kika magance shi
Aziza Idris: Tabbas
na fuskanci matsalar kasuwa kamar yanda yawanci marubuta suke fuskanta abinda
muke kira "Kanta waye" sai a karbi kayanka ba kudi ba kaya.
Shikenan a karo na gaba sai an sake zuba wani jari sannan abin zai motsa. Bayaga
haka da farko ban samu horaswa ba a fagen rubutu don haka a daki nake rufe
kaina nayi rubutu iya son raina. Lokacin da na fuskanci muhimmancin bincike a
rubutu lokacin ne nima kaina zan san na rubuta abun nunawa duniya domin ta. Karba
ta amfana kuma da shi. Wadannan dai sune matsalolin da ma fuskanta. Amma
alhamdulillah yanzu na daina dunkula littafai na bawa mutum daya da ni da mai
dab'ina muke aikin rabawa jahohi daban-daban a kasuwanninsu domin gano inda
matsalar take. Tunda muka canza tsari kuwa an samu ci gaba Alhamdulillah.
Mujallar Fikra: Kasancewarki
marubuciyar littafan hausa har ma da na turanci, wani shawara zaki ba Yan
uwanki marubuta akan cigaban rubutun Hausa
Aziza Idris:
Shawarar da zan bawa marubatanmu na hausa shine ya kamata mu fadada tunaninmu;
kamar yanda da yawa yanzu ana kokari gaskiya wuri farfado da hikimar rubutu ta
bangaren bincike haka ya kamata ace a fadada fagen rubutun. Duk da a tasowa an
saba da littafan soyayya ne suka fi sayuwa sai ayi amfani da hakan a hikimance
wurin shigo da sauran nau'ukan labarai wanda suka shafi fagen raha, ban tsoro,
labaran abin mamaki ko almara (fantasy), labarai masu zaburarwa da kuma saka
taraddadi (mystery/thrillers) da dai sauransu. Sannan mu yi kokari labaranmu
kar su tsaya akan bugu kawai yanda yanar gizo ya baza ko ina ya kamata haka
rubuce-rubucenmu suka zagaya yanda sauran kasashe dama wasu sassa na kasarnan
suke yi.
Mujallar Fikra: Ya
zaki haɗa rubutun hausa da na sauran kasashe,?
Aziza Idris: A
gaskiya an tsere mana nesa ba kusa ba, sai dai muyi la'akari da idan an
jinginamu tare dasu su tsofaffin hannune a harkar; sai dai yanda nake hangowa
marubuta hausa ma mun dauki hanyar isa inda wadannan mutane suka kai har ma a
dama damu.
Mujallar Fikra: Wani
taimako kike ganin sarakunan arewa da gwamnatin arewa ya kamata su ba rubutu da
marubuta Hausa
Aziza Idris:
Makaranta littafai sun hada kaso mafi yawa ne daga cikin matasa; saboda haka
yanda gwamnati take son kawo canji a al'umma to marubuta sune mafi kusanci da
matasa wanda suke iya canza musu tunani. Inaga Idan da gwamnati zata
tallafawa marubuta ta bangaren kare hakkokinsu da ma bada tallafin kayan aiki
to da ba karamin ci gaba za a samu al'umma ba. Domin da yawa za a samu
mutum nada basira da baiwa ta rubutu amma rashin samun goyon baya ko kuma yanda
za ayi da kayan da akayi aikinsu sai ya dakufar da marubuci. Har ila yau
taimakon harkar rubutu shima farfado da bangaren hikayace da zai samar da kofar
ayyuka ga matasa a kasar gabaki daya. Masarautu suna nasu kokarin don kamar
Gombe inda na fito duk inda kuka kai maganar matasa da harkar rubutu, to mai
martaba a shirye yake da ya saurareku ya kuma bada tasa gudumawar.
Haka nan wasu gwamnatotin
misali jahar Kaduna da dai sauransu.
Mujallar Fikra: Kasancewarki
marubuciya Madubin Al'umma wani shawara zaki ba ma'aurata da masu shirin yin
aure don su tsira da aurensu ganin cewa babban matsalar da ke damun al'umma
rikicin gidan aure ne da yawan mutuwar aure
Aziza Idris:
Babban shawarar da zan bawa mutane dangane da aure shine; Kuyi don Allah,
muddin aka dauki aure a matsayin bautar Allah to za a samu natsuwar gudanar da
rayuwar auren gaba daya.Sannan ya zama lallai sai da hakuri a cikin wannan
rayuwar da kuma asalin fahimtar juna. Ta bangaren mace akwai bukatar ta
bawa mijinta girma domin girmamawa shine abu na farko da zai saya miki
darajarki a idanun miji. Idan kina so mijinki ya rinka ganin darajarki
kema ya zamo lallai ki ga darajarsa. Ki kasance mai biyayya domin neman
aljannarki akan abinda duk bai sabawa shari'a ba.
A bangaren maza kuma ya kamata su san mata mutanene
masu rauni wanda ba abunda suka fi bukata komai ilimin mace komai kudinta da
mukaminta tana son tallafawa da tarairaya. Mata are emotional duk inda aka ce
kana kula da ita kana bata darajarta a matsayinta ta mutum, kana tallafa mata a
lokutan shiganta wasu hali; to duk abunda kace ko kan kace ma zata aikata na
kyautatawa gareka.
Shawara ga duka ma'aurata kuma shine yana da
matukar muhimmanci a daina daukaka laifi, duk lokacin da miji ko mata kuka
batawa juna rai ku tabbata ba ku yi bacci da bakin cikin juna ba, ku fito dashi
a daren a warware batu kowa ya huce a wuce wurin mai bada hakuri ya bada mai
amsar laifi ya amsaa ko kece da gaskiya amsa a wuce wurin ko itace da laifi
nuna mata a sannu a hankali. Kar fa a manta Allah ya sanya kauna da rahama
(natsuwa) a tsakanin ma'aurata.
Wannan kadai ya isa ya nuna mana darajar aure a
musulunci lokaci yayi da za a farga a nemi ilimin zaman rayuwa gaba daya
musamman na zamantakewar aure. Sai an samu ilimi za a tsira.
Mujallar Fikra: Me zaki ce da masoyanki?
Aziza Idris: Ina Kaunarsu Fisabilillahi
Mujallar Fikra: Mun gode Hajiya Aziza
Aziza Idris: Nima Na gode
Comments
Post a Comment