Marubuci idon al'umma ~ Ummu-Abdoul
MARUBUCI IDON AL'UMMA
Safiyyah Ummu-Abdoul
safiyyahjibril@gmail.com
Al'umma kan k'aru ta fannoni da dama daga Alkalamin marabuci. Mai rubutu ba zai kasance marubuci ba har sai ya kasance ido ga al'umma idon da ba makauniyar ido ba.
Yana da kyau kafin ka fara rubutu ka yi tunanin shin shahara kake nema a wajen al'umma ko kuma shahara kake nema a wajen Ubangijinka. Sau da yawa marubuta kan manta cewa yanda rubutun su kan samar musu soyayya a idon jama'a hakan zai iya sama musu soyayyar Allah har ta zama sanadin shigar su Aljanna. Amma kuma hakan ba yana nufin shi marubuci malami ne ta fuskar addini ba, hakan ba zai sa ya zama masanin kimiyyar siyasa ko tattalin arziki ba da har zai ga ai yana da lasisin yanke hukunci ta wannan fannin matukar ba ya kasance mai ilimi akan wannan fannin ba.
Kasancewar ka idon Al'umma hakan bai sa dole duk abin da ya fito daga bakinka ya zama shi ne daidai ba da har dole in ba'a bi ra'ayin ka ba toh mutane sun ɓata. Abin da ya kamata ka sani shi ne kai ɗin ma mutum ne kamar kowa, ba kuma komai zai bambanta ka da mutane ba sai ka kasance mai zurfin ilimin Addini har ma da na zamani. Hakan zai sa ka zama mai rubutu yanda zai amfani jama'a.
Ra'ayinka fa ra'ayinka ne, zai iya zama daidai zai iya zama kuskure saboda rubutu bai baka lasisin zama maasumi ba.
Idan mu ka duba shaharrarun marubuta da har bayan babu su ana karanta littafan su, zamu iske sun zama idon al'umma ne ta hanyar amfani da fikrar da Allah ya basu wajen ilmantar da al'umma cikin nishadantarwa, wannan kuma ya siyan musu shahara ba don sun nema ba.
Amma wasu daga cikin marubutan wannan zamani suna rubutu ne don neman shahara, hakan ya sa maimakon su ilmantar sai su ɓatar ko kuma garin ilmantarwa sai su nuna matsayin su na masu karamin ilimi. Hakan kuma na faruwa ne a dalilin rashin neman ilimi akan jigon da su ke son ilmantarwa.
Wasu kuma daga sun fitar da littafi kasuwa gani suke ai duniya babu kamarsu, babu ruwan su da damuwa da shin akwai sakon da ya iske al'umma a cikin littafin ko kuma baɗalar da suka sanya ya aika fasadi ga al'umma.
Wasu kuma daga sun iske abokan su a shafin Facebook ya kai matakin dubu huɗu zuwa sama nan zaka same su da ganin ai sun kai matakin da zasu yanke hukunci a fannin addini da shari'a. Hakan ba shine matsayin ka na marubuci ba sai dai in har bayan rubutu kana da matsayin malanta.
Akwai marubuta da dama da suka amsa sunan idon duniya gaba ɗaya don duk abin da zai fito daga garesu zaka iske ba ra'ayin su bane zallan ilimi ne don fadakar da al'umma.
Da haka nake kira ga marubatanmu na Kasar Hausa da mu zama masu tafiya da zamani ta fuskar ilimi. Hakan zai hana ku zama makauniyar ido ga al'umma.
Ina kira ga manyanmu ta fuskar rubutu don farfesoshin da ke ciki sun fi gaban a kirga su, da su samar da hanyar tallafawa marubuta don samun ilimin gaba da sakandire, wa'inda ba su da shahadar kammala sakandire a tallafa musu da kuɗin jarrabawar Waec da Neco, sannan a nusar da su Mahimmancin neman ilimin muhammadiyya don samun gyara da cigaban Adabin hausa.
Safiyyah Ummu-Abdoul
15/10/2017
Comments
Post a Comment