AURE BAUTAR ALLAH CE BA BAUTAR MIJI BA
Daya daga cikin matsalolin aure a Nahiyar Afirka Shine ɗaukan aure a matsayin bautar Miji tun da hadisi ya zo akan Aljannar mace yana karkashin kafar mijinta maimakon su yi amfani da kasancewar sa tsani zuwa ga Aljanna ta hanyar kyautata masa don samun yardan Allah
Da ace iyaye suna faɗakar da ya'yansu Mahimmancin yin komai da ya shafi zamantakewar aure a matsayin ibada da mazaje ba za su cutar da matan da suka aura ba sannan mata ba zasu gaji da yi ma mazajen su biyayya ba saboda ban taɓa jin an ce an gaji da yi ma ALLAH biyayya ba.
Yana daga cikin Al'adunmu in za'a aurar da mace ayi ta kira mata hakuri, ni a gani na ba hakuri kawai ya kamata a kira mata ba sai a kara da ta ji tsoron Allah sannan ki nemi yardan Allah. Don abubuwa ukun nan shine sirrin zaman lafiya a gidan aure.
Bayan kalmar Hakuri da ake ambata mata sai kuma cusa ma yarinyar ra'ayin in ba ta bi mijinta ba zai sake ta, ko zai kara aure ko kuma zai bi kadangarun bariki, abin mamaki kuma sai ta yi ɗin kuma ya dankara mata saki ko ya kai ga shigo da karuwa har cikin gida.
Amma da zarar ma'aurata suna tafiyar da rayuwar su a matsayin bautar Allah, za su yi komai ne don neman yardan Allah kuma duk wanda Allah ya yarda da shi ya so shi babu wani halitta da zai iya wulakanta shi
Duba da yanda masu siyar da magungunan mata don kyautatawa mazajen aure su ka yawaita haka sakin aure ya yawaita. Don ko wacce mace burinta ta mallaki mijinta, kada mijinta ya wulakanta ta kada a sake ta, kuma ta zama abin so da kauna a idon mijinta. Hakan ya sa sai su koma ga shawarar iyaye na in ka kyautata ma miji zai kyautata maka, in yaji daɗi zaki mallake shi maimakon su yi kyautatawan a matsayin ibada don neman yardan Allah sai su saɓa ma Allah don neman yardan miji ta ya hakan zai kai ga nasara.
Ya kamata Iyaye da maluman addini su chanza salon wa'azin aure, a nusar da mazaje da mataye Mahimmancin yin ibada don Allah, domin duk. Bautan da aka yi don wani toh Riya ce ciki kuwa har da aure. Maza su sa a ransu in sun kyautata don Allah su ka yi in kuma sun munana duk sakamako na wajen Allah. Hakan zai rage yawan matsalolin aure da ake fuskanta musamman a arewacin Nijeriya.
Safiyyah Ummu-Abdoul
Safiyyahjibril@gmail.com
22/09/2017
Comments
Post a Comment