Posts

Showing posts from October, 2017

YAWAN 'DAUKAKA LAIFI DA MA'AURATA KE YI YA FI KOMAI HADDASA SAKIN AURE- Azeeza Idris

Image
Azeeza Idris  wacce aka fi sani da Ummyasmeen  musamman a kafar sadarwa ta Instagram da kafar karanta littatafai ta duniyar gizo wato Wattpad. Marubuciya ce da tauraronta ke haskawa saboda d’umbin fikrar da Allah ya ba ta. Ta ci sarauniyar Marubuta Nigeria a Duniyar Wattpad sannan tana da dubban Makaranta littafanta daga ko ina a fad’in duniyar nan. Ba a rubutu kad’ai ta shahara ba har ma da fannin girke-girke. Ga hirarta da Mujallar Fikra.. Mujallar Fikra:          Assalamu Alaikum warahmatullah Aziza Idris :               Wa’alaikumus salam Wa Rahmatullah Mujallar Fikra:         Za mu so sanin wacece Umm Yasmeen Aziza Idris :               Masha Allah, da farko dai sunana Azizah Idris Muhammad. An haife ni a jihar Bauchi a ranar 06/10/1988. Amma ni asali 'yar jihar Gombe ce daga karamar hukumar Yamaltu/Deba.  Nayi karatun  firama...

Marubuci idon al'umma ~ Ummu-Abdoul

Image
MARUBUCI IDON AL'UMMA Safiyyah Ummu-Abdoul safiyyahjibril@gmail.com Al'umma kan k'aru ta fannoni da dama daga Alkalamin marabuci. Mai rubutu ba zai kasance marubuci ba har sai ya kasance ido ga al'umma  idon da ba makauniyar ido ba. Yana da kyau kafin ka fara rubutu ka yi tunanin shin shahara kake nema a wajen al'umma ko kuma shahara kake nema a wajen Ubangijinka. Sau da yawa marubuta kan manta cewa yanda rubutun su kan samar musu soyayya a idon jama'a hakan zai iya sama musu soyayyar Allah har ta zama sanadin shigar su Aljanna. Amma kuma hakan ba yana nufin shi marubuci malami ne ta fuskar addini ba, hakan ba zai sa ya zama masanin kimiyyar siyasa ko tattalin arziki ba da har zai ga ai yana da lasisin yanke hukunci ta wannan fannin matukar ba ya kasance mai ilimi akan wannan fannin ba. Kasancewar ka idon Al'umma hakan bai sa dole duk abin da ya fito daga bakinka ya zama shi ne daidai ba da har dole in ba'a bi ra'ayin ka ba toh mutane sun ɓata. ...