Posts

Showing posts from September, 2017

YA KAMATA GWAMNATOCIN AREWA SU TALLAFA WA RUBUTU DA MARUBUTA HAUSA ~ AUYO

Image
Auyo matashin marubuci ne da yayi tashe a lokacinsa, salon rubutunsa ya sha bambam da rubutun mafi akasarin Marubuta. ya fara rubutu tun yana da shekara goma sha uku a duniya kuma har ila yau yana rubutu mai cike da fad'akarwa, ilmantarwa gami da Nishad'antarwa. Littafinsa HISABI na d'aya daga cikin tarin littafan da Makaranta ke tsumaye. Ga hirarsa da Mujallar Fikra *** Mujallar Fikra :             Assalamu Alaikum warahmatullah Auyo :                            Waalaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu Mujallar Fikra :            Zamu so mu ji takaitaccen tarihinka   Auyo :                       Cikakken sunana Abubakar Muhammad . An haife Ni a garin Auyon Jiha...

AURE BAUTAR ALLAH CE BA BAUTAR MIJI BA

Image
Daya daga cikin matsalolin aure a Nahiyar Afirka Shine ɗaukan aure a matsayin bautar Miji tun da hadisi ya zo akan Aljannar mace yana karkashin kafar mijinta maimakon su yi amfani da kasancewar sa tsani zuwa ga  Aljanna ta hanyar kyautata masa don samun yardan Allah Da ace iyaye suna faɗakar da ya'yansu Mahimmancin yin komai da ya shafi zamantakewar aure a matsayin ibada da mazaje ba za su cutar da matan da suka aura ba sannan mata ba zasu gaji da yi ma mazajen su biyayya ba saboda ban taɓa jin an ce an gaji da yi ma ALLAH biyayya ba. Yana daga cikin Al'adunmu in za'a aurar da mace ayi ta kira mata hakuri, ni a gani na ba hakuri kawai ya kamata a kira mata ba sai a kara da ta ji tsoron Allah sannan ki nemi yardan Allah. Don abubuwa ukun nan shine sirrin zaman lafiya a gidan aure. Bayan kalmar Hakuri da ake ambata mata sai kuma cusa ma yarinyar ra'ayin in ba ta bi mijinta ba zai sake ta, ko zai kara aure ko kuma zai bi kadangarun bariki,  abin mamaki kuma sai ...